IQNA

Zagon Karatun Sanin Tajwidi Da Fannonin Kur'ani A Kutaib

15:28 - October 12, 2010
Lambar Labari: 2011594
Bangaren kasa da kasa; cibiyar ilimin kur'ani a garin Ummul Hamam a lardin Kutaib na kasar Saudiya ta fara kaddamar da zangunan karatu da bada horo kan ilimin tajwidi da sauran fannoni na kur'ani a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto daga gidan watsa labarai na Rasid ya watsa rahoton cewa' cibiyar ilimin kur'ani a garin Ummul Hamam a lardin Kutaib na kasar Saudiya ta fara kaddamar da zangunan karatu da bada horo kan ilimin tajwidi da sauran fannoni na kur'ani a yankin. Wannan zangunan bada horo na karatun tajwidi da sauran fannoni na ilimin Kur'ani wata babbar dam ace ga duk wanda yake bukata da sha'awar samun ilimi da horo kan fannonin kur'ani mai girma.

672792
captcha