Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na almuslim an bayyana cewa, wata masaniya musulma a kasar Spain ta bayyana cewa akasarin mutanen da suke rayuwa a cikin kasashen nahiyar turai ba su da wata masaniya kan addinin muslunci, wanda haka ne ya sanya su gaba da shi bisa jahilcinsa.
Wannan masaniya wadda balaba ce 'yar kasar Iraki da ke zaune a kasar Spain ta bayyana hakan ne a wani zaman taro da aka gudanar a birnin Madrid fadar mulkin kasar Spain dangane da matsayin Musulunci kan rayuwar zamantakewar al'umma.
Ta ce jahilci dangane da addinin muslunci shi ne bababn abin da ya jefa al'ummomin kasashen yammacin turai cikin tsananin gaba da addinin muslunci, wanda da sun san koyarwarsa da sun zama a gaba wajen karbarsa.
681225