IQNA

Sanin Kur'ani Shi Ne Darasi mafi Muhimmanci Ga Dalibai

10:48 - October 27, 2010
Lambar Labari: 2020639
Bangaren harkokin kur'ani: A yau babu wani abu mafi muhiommaci da alfano ga dalibai kamar darussan da suka shafi Alkur'ani mai girma.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran daga reshensa na birnin Qum ya watsa rahoton cewa; A yau babu wani abu mafi muhiommaci da alfano ga dalibai kamar darussan da suka shafi Alkur'ani mai girma. Ayatullahi Muhammad Taki Musbahu Yazdi shugaban bangaren koyarwa da gudanar da bincike ta imam Khomeini ® a ranar uku ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a lokacin da yake bayani kan darussan da suka shafi ilimomon Kur'ani mai girma a wannan mu'assisar ya bayyana cewa; domin bada amsa shibhohi da tambayoyi ya fayyace cewa dogaro da kur'ani dole ya kasance yana tafiya kafada da kafada da sunnar ma;aiki ingattacciya.


683002
captcha