IQNA

16:56 - October 27, 2010
Lambar Labari: 2021038
Bangaren kasa da kasa, Duk da fatawar da jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Ozma sayyid Ali Khamenei ya bayar da ke kira zuwa ga hadin kan musulmi ta hanya girmama mutanen da 'yan sunna ke girmamawa, amma tashar Aljazira na ci gaba da hankoron kawo rarraba tsakanin musulmi.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na iba an bayyana cewa, duk da fatawar da jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Ozma sayyid Ali Khamenei ya bayar da ke kira zuwa ga hadin kan musulmi ta hanya girmama mutanen da 'yan sunna ke girmamawa, amma tashar Aljazira na ci gaba da hankoron kawo rarraba tsakanin musulmi mabanbantan mazhabobi.

Fatawar da jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar da ke kira zuwa ga girmama wadanda 'yan sunna suke girmamawa, wanda hakan ya samu karbuwa daga manyan malaman sunna, amma tashar aljazira tana ci gaba da kokarin kawo baraka tsakanin musulmi sunna da shi'a.

A cikin makon nan ne tashar aljazira ta kira shahararren bawahabiya nan Muhammad Uraifi, da nufin bayyana sukar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah, ta yadda hakan zai harzuka daya bangaren musulmi a kan dayan.

682901Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: