Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; Ramziya Cilik masaniya harkokin kur'ani a Turkiya ta bukaci mahukumtan Iran da jami'ai na su tallafawa harkokin kur'ani a kasar ta Turkiya da kuma jinjinawa mahukumtan na jamhuriyar Musulunci ta Iran kan wannan goyan baya da gudummuwar da suke bayarwa. Malamar ta fadi haka ne a lokacin wata tattaunawa da ta yi dad an jaridar kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran.
684902