Bangaren kasa da kasa; mu'assisar kur'ani ta Alshatubi a Koweiti ta bude cibiyar koyar da hardar Kur'ani ta goma da ke karkashin wannan mu'assisar ga mata kuma a ranar sha daya ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a yankin Aljahra na wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga jaridar Aljaridatu da ake buga ta a kasar Koweiti ya watsa rahoton cewa; mu'assisar kur'ani ta Alshatubi a Koweiti ta bude cibiyar koyar da hardar Kur'ani ta goma da ke karkashin wannan mu'assisar ga mata kuma a ranar sha daya ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a yankin Aljahra na wannan kasa.Khalid Abu Gais shugaban ofishin kula da harkokin kur'ani mai girma a ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Koweiti daga cikin jawabin budewa day a kaddamar ya bayyana cewa; wannan mu'assisar ta haradar kur'ani Alshatubi tana taka rawar gani wajen yayewa da horar da kwararru ta fuskar hardar kur'ani mai girma.
705526