Bayan hare-haren da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma wani yanayi da makiya juyin juya halin Musulunci suke kokarin haifar da yanke kauna da raunana rudin al'ummar Iran ta hanyar makirci iri-iri, kamfanin dillancin kur'ani na kasa da kasa (IKNA) ya kaddamar da gangamin "Fatah" na kur'ani.