Bangaren kasa da kasa, An kawo karshen mataki na farko na gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, tare da halartar daruruwan makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar sharq an bayyana cewa, An kawo karshen mataki na farko na gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, tare da halartar daruruwan makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki na kasar ta Qatar.
Wadanda suka dauki nauyin gudanar da shirin wannan gasa daga cibiyoyin kur'ani 29 daga sasasn kasar sun bayyana cewa, kimanin dalibai 550 ne suka shiga cikin shirin a mataki na farko, inda daga bsani kuma za a sanar da sunayen wadanda za su wuce zuwa ga mataki na gaba.
Kawo karshen mataki na farko na gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar, tare da halartar daruruwan makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki.
717435