IQNA

Shugaban Bangaren Kaninkanci Na Kamfanin Microsoft Zai Ziyarci Cibiyar Nur

18:38 - January 13, 2011
Lambar Labari: 2063957
Bangaren kasa da kasa, Shugaban bangaren ayyukan kanikanci na babban kamfanin nan na yanar gizo na microsoft zai ziyarci cibiyar na’ura mai kwakwalwa ta nur da ke birnin Qom a cikin jamhuriyar musulunci ta Iran, da ke gudanar da ayyukan bincike da nazarin ilmomi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Qom an habarta cewa, shugaban bangaren ayyukan kanikanci na babban kamfanin nan na yanar gizo na microsoft zai ziyarci cibiyar na’ura mai kwakwalwa ta nur da ke birnin Qom a cikin jamhuriyar musulunci ta Iran, da ke gudanar da ayyukan bincike da nazarin ilmomin addini da sauransu.
Babban jami’in na kamfanin microsoft zai ziyarci babban ofishin cibiyar ta Nur ne a cikin wannan mako, inda zai gana da jami’an da ke kula da bangaren zartarwa na cibiyar, daga nan kuma zai duba irin muhimman ayyukan da ake gudanarwa awurin, tare da bayar da shawarwari kan yadda ayyuakn suke gudana a wannan babbar cibiya ta na’ura mai kwakwalwa.
Ziyarar shugaban bangaren ayyukan kanikanci na babban kamfanin nan na yanar gizo na microsoft a cibiyar na’ura mai kwakwalwa ta nur da ke birnin Qom a cikin jamhuriyar musulunci ta Iran, da ke gudanar da ayyukan bincike da nazarin ilmomi, za ta bude wani sabon shafin dangantaka tsakanin bangarorin biyu.
728954


captcha