Bangaren siyasa da zamantakewa;Ayatullahi Kablan a ranar sha takwas ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a lokacin wata ganawa da tawagar jabahatul Demokradiya don intar da Palasdinu a birnin Beirut ya jaddada samar da hadin kai a tsakanin Palasdinawa domin fuskantar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; Ayatullahi Kablan a ranar sha takwas ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a lokacin wata ganawa da tawagar jabahatul Demokradiya don intar da Palasdinu a birnin Beirut ya jaddada samar da hadin kai a tsakanin Palasdinawa domin fuskantar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila.A ci gaba da jawabin nasa ayatullahi Kablan ya kara da cewa;larabawa da musulmi ya zama wajibi su rungum,I addininsu da aiki da hankali wajan kalubalantar haramtacciyar kasar Isra'ila a matsayin kashin bayan yan mulkin mallaka a wannan zamani da muke ciki da kuma hakan zai kawo karshen makirci da zagon kasa da take kullawa musulmi a duniya baki daya.
744166