IQNA

Imam Husaini (AS) a cikin kur’ani / 4

Raja'ah Imam Husaini Cigaban Taimakon Allah ga Annabawa da Muminai

15:38 - July 08, 2025
Lambar Labari: 3493512
IQNA – Taimakon Allah yana bayyana ta hanyoyi daban-daban ga annabawa da muminai.

Tunda Imam Husaini (AS) ya yi shahada bisa zalunci a Karbala, taimakon Ubangiji yana ci gaba da dawowansa (Raja'a) a nan duniya.

A ranar Ashura, a hudubarsa ta karshe Imam Husaini (AS) ya bayyana cewa;

"Ni ne farkon wanda kasa za ta tsaga gare shi, kuma zan fito - fitowar da ta yi daidai da fitowar Amirul Muminina (AS) [Imam Ali], da tashin Qa'immu [Mahdi da ake jira (Allah ya gaggauta masa bayyani), da kuma rayuwar Manzon Allah (SAW)."

Imam Sadik (AS) ya ce: “Na farkon wanda kabari zai tsage masa, kuma wanda zai girgiza kurar da ke kansa, shi ne Husaini bn Ali (AS) zai tashi da mabiya dubu saba’in da biyar (mabiya)”.

Sannan ya kawo wadannan ayoyi guda biyu na Alqur'ani:

"Lalle ne, Muna taimakon manzanninMu da wadanda suka yi imani da rayuwar duniya, da ranar da shaidu ke fitowa, ranar da uzurin azzalumai ba zai amfane su ba, kuma an la'ane su, kuma suna da mafi sharrin gida." (Aya ta 51-52 cikin suratul Ghafir).

Kur'ani akai-akai yana magana akan taimakon Allah ga annabawa da muminai. Ga wasu misalai:

Taimako ga Nuhu (AS):

"Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi a cikin jirgin." (Suratul Shuara aya ta 119).

Taimako ga Ibrahim (AS):

Muka ce wa Wuta, ‘Ki yi sanyi, ki natsu (da Ibrahim)’ (Suratu Anbiya, aya ta 69).

Taimako ga Lutu (AS):

"A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, shi da mutãnensa gabã ɗaya, fãce matarsa." (Suratul Hijir aya ta 59).

Taimako ga Yusuf (AS):

"Kuma kamar wancan ne Muka sanya Yũsufu a cikin ƙasa, yanã zama inda ya so." (Suratul Yusuf aya ta 56).

Taimako ga Shu'aibu (AS):

"Kuma a lokacin da umurninMu ya zo, Muka kubutar da Shu'aibu saboda rahamarMu, tare da wadanda suka yi imani." (Suratul Hud aya ta 94).

Taimako ga Salih (AS):

"Kuma a lokacin da umurninMu ya je, Muka kubutar da Salihu tare da wadanda suka yi imani tare da shi saboda rahamarMu." (Suratul Hud aya ta 66).

Taimako ga Hud (AS):

"Kuma a lokacin da umurninMu ya je, Muka kubutar da Hudu tare da wadanda suka yi imani tare da shi saboda rahamarMu." (Suratul Hud aya ta 58).

 

 

 

 

3493713

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: imani rahama taimako rayuwa duniya mabiya
captcha