IQNA

Hudubar Juma'a a Masallacin Harami da aka fassara zuwa harsuna 35

22:45 - July 05, 2025
Lambar Labari: 3493504
IQNA - A karon farko an tarjama hudubar juma'a ta wannan makon a babban masallacin juma'a zuwa harsuna 35.

Hukumar kula da harkokin addini ta Masallacin Harami da Masallacin Manzon Allah (S.A.W) ta sanar a farkon wannan makon cewa za a fassara hudubar Juma'a ta wannan makon zuwa harsuna 35 a karon farko, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito.

Manufar ita ce a arzurta maziyartai da mahajjata tare da bayyana kyawawan halaye da ladubban sallar Juma’a.

Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais ne zai jagoranci Sallar Juma'a a wannan makon.

Fahim Al-Hamid, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin addini kuma shugaban yada labarai da sadarwa a hukumar kula da harkokin addini, ya jaddada kudirin cibiyar na fassara hudubar Juma’a zuwa harsuna da dama, a matsayin wata gada ta sadarwa tsakanin mutane da musayar al’adu da wayewa.

Hukumomin Saudiyya na kallon tarjamar hudubar Juma'a a matsayin hidima ga maziyarta da mahajjata da ke magana da harsuna daban-daban.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4292537

 

captcha