Bangaren siyasa da zamantakewa, Wasu daga cikin mutanen kasar Labanan sun gudanar da wani ganngami a gaban ofishin majalisar dinkin duniya, domin nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar palastinu da ke karkashin danniyar yahudawan sahyuniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar tashrin da ake bugawa akasar Syria an habarta cewa, wasu daga cikin mutanen kasar Labanan sun gudanar da wani ganngami a gaban ofishin majalisar dinkin duniya, domin nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar palastinu da ke karkashin danniyar yahudawan sahyuniya tsawon shekaru.
Wannan gangami dai ya hada kungiyoyi ne daban-daban na mutanen kasar Labanan, wadanda suke nuna rashin amincewarsu da siyasar zalunci dadanniya ta yahudawan sahyuniya kan al’ummar palastinu, wanda kuma yin gangamin a gaban ofishin majalisar dinkin duniya yana da babban sakonsa.
Wasu daga cikin mutanen kasar Labanan sun gudanar da wani ganngami a gaban ofishin majalisar dinkin duniya, domin nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar palastinu da ke karkashin danniyar yahudawan sahyuniya na haramtacciyar kasar Isra’ila.
746287