IQNA

18:44 - February 21, 2011
Lambar Labari: 2084269
Bangaren siyasa, Daya daga cikin mabobin cibiyar da ke shirya tarukan malaman addinin muslunci ya bayyana cewa, yada koyarwar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a tsakanin al'ummar musulmi na daga cikin muhimman dalilan shirya tarukan makon hadin kai.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada wakilin kamfanin dillancin labaran iqna daya daga cikin mabobin cibiyar da ke shirya tarukan malaman addinin muslunci ya bayyana cewa, yada koyarwar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a tsakanin al'ummar musulmi na daga cikin muhimman dalilan shirya tarukan makon hadin kai na musulmi.

Ahmad salik ya sheda cewa, manzon Allah (SW) shi ne jigo na hadin kan dukkanin musulmi, kuma yin koyi da abin da ya zo da shi shi ne bababn abin da zai hada kan musulmi, haka nan kuma yin aiki da abin da iyalan gidansa suka yi shi ne babban abin da ke tabbatr da cewa ana yin sahihin koyi da koyarwarsa.

Ya ce hadin kai tsakanin al'ummar musulmi wajibi ne musamman a wannan zamani da musulmi suke fuskantar babban kalu bale daga makiya, wanda kuma da samun baraka ko rarrabar kai a tsakaninsu, zai ci gaba da bawa makiya dammar nisanta sauran al'ummomin daga fahimtar hakinain koyarwar musulunci.

Daya daga cikin mabobin cibiyar da ke shirya tarukan malaman addinin muslunci ya bayyana cewa, yada koyarwar iyalan gidan manzon Allah (SAW) a tsakanin al'ummar musulmi na daga cikin muhimman dalilan shirya tarukan makon hadin kai.

750472

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: