IQNA

Taro Mai Taken Manzon Allah (SAW) Abin Koyi Ga Gabaci Da Yammcin Duniya

10:35 - March 03, 2011
Lambar Labari: 2089503
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taro mai take manzon Allah Muhammad (SAW) abin koyi ga al’ummomin gabaci da yammacin duniya a birnin Cambrige na kasar Birtaniya, wanda cibiyar shirya tarukan karawa juna sani kan addinin musulunci za ta gudanar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na MEOC cewa, za a gudanar da wani zaman taro mai take manzon Allah Muhammad (SAW) abin koyi ga al’ummomin gabaci da yammacin duniya a birnin Cambrige na kasar Birtaniya, wanda cibiyar shirya tarukan karawa juna sani kan addinin musulunci da ke birnin.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan zaman taron zai samu halartar manyan malamai da masana daga sassa daban-daban na kasar Birtaniya, inda za agabatar da laccoci kan matsayin manzon Allah (SAW) da kuma abubuwan da ya yi wadanda suke gudunmawa ce ga rayuwar bil adama a dukkanin bangarorinta matukar aka yi koyi da ita.
Gudanar da zaman taron mai take manzon Allah Muhammad (SAW) abin koyi ga al’ummomin gabaci da yammacin duniya a birnin Cambrige na kasar Birtaniya, wanda cibiyar shirya tarukan karawa juna sani kan addinin musulunci ta birnin za ta dauki nauyinsa na da matukar muhimmanci.
756533


captcha