IQNA

Wakilin Jagoran Juyin Musulunci Ya Yi Kira Da A Saki Liman Juma'a Na Katif A Saudiyya

18:15 - March 07, 2011
Lambar Labari: 2092001
Bangaren kasa da kasa, Daya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci kuma daga cikin jagororin mabiya tafarkin manzon Allah (SAW) wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci a garin katif, ya yi kira ga mahukuntan Saudiyya da su gaggauta sakin limamin birnin.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin saarwa na yanar gizo na tashar rasid an bayyana cewa, daya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci kuma daga cikin jagororin mabiya tafarkin manzon Allah (SAW) wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci a garin katif, ya yi kira ga mahukuntan Saudiyya da su gaggauta sakin limamin birnin na Katif da ke gabacin kasar saudiyya.

Malam Abdulkarim Al-habil wanda kuma shi ne limamin masallacin juma'a na Al-rubaiya ya bayyana cewa, babu wani dalili na ci gaba da rike malam Taufik Amiri, saboda kawai ya yi kira da a mayar da tsarin kasar kan tafarki sarauta ta kundin tsarin mulki.

Y ace ci gaba da tsare malamin da mahukuntan kasar Saudiyya suke yi ba maslaha ne gare sub a, kuma wajibi ne su gaggauta sakinsa matukar dai suna fatan ganin an zauna lafiya tsakaninsu da al'ummar yankin.

758561

captcha