Bangaren kasa da kasa, an dakatar da buka kur’ani mai tsarki a babbar cibiyar sarki Fahad da ke birnin Madina mai alfarma, wadda ita ita ce cibiya mafi girma da ke buga kwafin kur’ani a kasar Saudiya, sakamakon shiga yajin aiki da ma’aikatan cibiyar suka yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muhit an bayyana cewa, an dakatar da buka kur’ani mai tsarki a babbar cibiyar sarki Fahad da ke birnin Madina mai alfarma, wadda ita ita ce cibiya mafi girma da ke buga kwafin kur’ani a kasar Saudiya, sakamakon shiga yajin aiki da ma’aikatan cibiyar suka yi a cikin makon nan da muke ciki.
Bayanin ya ci gaba da cewa, Mahukuntan kasar Saudiyya sun yi iyakacin kokarinsu wajen ganain sun gamasar da ma’aikatan wannan cibiya domin kada suka shiga yajin aiki, amma kokarin bai haifar da da mai ido ba, inda daga karshe dai ma’aikatan suka shiga yajin aikin, wanda ya yi sanadiyar tsayawar dukkanin ayuukan cibiyar cak.
Dakatar da buka kur’ani mai tsarki a babbar cibiyar sarki Fahad da ke birnin Madina mai alfarma, wadda ita ita ce cibiya mafi girma da ke buga kwafin kur’ani a kasar Saudiya, sakamakon shiga yajin aiki da ma’aikatan cibiyar suka yi, zai kawo koma baya matuka ga ayyukan da cibiiyar ta saba gudanarwa.
761599