IQNA

An Gudanar Gudanar Da Bukin Kammala Tilawar Kur’ani Mai Tsarki Ta Nur

15:33 - March 22, 2011
Lambar Labari: 2097826
Bangaren kur’ani, An gudanar bukin kammala tilawar kur’ani mai tsarkida ake yi wa lakabi da nur, wadda a ka gudanar a karo na hudu a daren karshe na shekarar hijira shamsiyya, wanda cibiyar Imam Jawad (AS) kan dauki nauyin gudanarwa a garin Khomeini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an gudanar bukin kammala tilawar kur’ani mai tsarkida ake yi wa lakabi da nur, wadda a ka gudanar a karo na hudu a daren karshe na shekarar hijira shamsiyya, wanda cibiyar Imam Jawad (AS) kan dauki nauyin gudanarwa a garin Khomeini dake tsakiya jamhuriyar musulunci.
A bangare guda kuma shugaban cibiyar kula da ayyukan kur’ani ta malayer ya bayyana cewa an bayar da takardun shedar kammala samun horon karatun kur’ani mai 180 ga dalibai da suka halarci wani shiri da cibiyar ta shirya gudanarwa, wanda ya samu nasara wajen samar da makaranta da suka halarci horon.
Ya ci gaba da cewa, wannan shiri da cibiyar ta aiwatar na daga cikin irinsa da cibiyoyin kur’ani suke aiwatarwa da nufin samar da makanta da mahardata a cikin al’ummar musulmi, wanda kuma hakan na samun karbuwa daga matasa da suke da sha’awar koyon karatu ko hardar kur’ani mai tsarki, kuma bayar da sakamako nashedar samun horon zai ta samu karbuwa ako’ina cikin kasashen musulmi da na larabawa.
765788


captcha