IQNA

19:51 - April 12, 2011
Lambar Labari: 2104866
Bangaren siyasa da zamantakewa, mataimakin shugaban majalisar koli ta mabiya mazhabar shi’a akasar Lebanon Ayatollah Sheikh Amir Qabalan ya jaddada wajabcin warware matsalar kasar Bahrain ta hanayar shigar malamai da kuma yin amfani da hikima da basira, maimakon yin amfani da bangaranci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na kasar Lebanon cewa, mataimakin shugaban majalisar koli ta mabiya mazhabar shi’a a kasar Lebanon Ayatollah Sheikh Amir Qabalan ya jaddada wajabcin warware matsalar kasar Bahrain ta hanayar shigar malamai da kuma yin amfani da hikima da basira, maimakon yin amfani da bangarancin mazhaba ko abin da ya yi kama da hakan.
Malamin ya ci gaba da cewa babu wani dalili da zai sanya mahukuntan Bahrain su fake da batun mazhaba domin murkushe masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi na siyasa akasar, tare da tabbatar da tsarin kama karya kansu, domin kuwa kowa aduniya ya san abin da ke faruwa ba shi da wata dangantaka da batun mazhaba kamar yadda gidanasarautar da masu kare daga kasashen larabawa suke rayawa.
Al’ummar kasar Bahrain sun mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu zanga-zanga a kasar baki daya. 772496
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: