IQNA

An Gudanar Da Zaman Tattaunawa Kan Tattalin Arzikin Musulunci A Kasar Lebanon

14:37 - April 20, 2011
Lambar Labari: 2109202
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman tattaunawa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, dangane da hanyoyin habbaka ttatalin arzikin kasashen muslumi da kuma yadda zai yi tasiri a cikin harkokin tattalin arziki na duniya, ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba.
Kamfanin dillancin labarn iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lorientlejour an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman tattaunawa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon, dangane da hanyoyin habbaka ttatalin arzikin kasashen muslumi da kuma yadda zai yi tasiri a cikin harkokin tattalin arziki na duniya, ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba.
A bangare guda kuma an fara gudanar da taron baje koli na kayan fasahar masana a musulunci a kasar Birtaniyam, wanda babbar cibiyar kula da kayan tarihin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa tun daga makon da ya gabata a babban dakin tarukanta da ke birnin London fadar mulkin kasar.
Taron yana samun halartar masana kan harkokin al’adu da tarihi daga jami’ar birnin London da kuma wasu cibiyoyi na mabiya addinin muslunci da ke cikin sassan kasar, haka nan kuma ana nuna wasu daga cikin abubuwan da aka samar na fasahar musulunci a kasar weadanda suke nuna kokarin masana musulmi masu fasaha da suke gudanar da ayyuka a wannan fage.
776905

captcha