Bangaren kasa da kasa, shugaban karamin ofishin jakadancin kasar Amurka a kasar Faransa ya nemi uzuri daga shugaban masallacin birnin Lion kan cin zarafin da wasu jami’an kasarsa suka yi ma al’ummar musulmin kasar Faransa, ta hanayar bayyana babban masallacin birnin Lyon da cewa ya zama wata babbar matattar ‘yan ta’adda.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafuin sadarwa na yanar gizo na wikiliks an bayyana cewa, wani jami’n Amurka ya zargi musulmin Faransa da cewa ‘yan ta’’adda ne, a kan shugaban karamin ofishin jakadancin kasar Amurka a kasar Faransa ya nemi uzuri daga shugaban masallacin birnin Lion kan cin zarafin da wasu jami’an kasarsa suka yi ma al’ummar musulmin kasar Faransa, ta hanayar bayyana babban masallacin birnin Lyon da cewa ya zama wata babbar matattar ‘yan ta’adda da ke da hadari.
A labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo an bayyana cewa, Mgr Podvin babban mai magana da yawun kwamitin anyan malaman addinin kirista a kasar Faransa ya yi kakkausar suka kan yadda gwamnatin kasar take tafiyar da siyasarta kan mabiya addinin muslunci kuma marassa rinjaye a kasar,inda ake nuna musu banbanci na zahiri.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na le-coran an bayyana cewa, an saka tarjamar kur’ani mai tsarki a cikin shafin yanar gizo a cikin harshen farasanci, tare da karatun kur’ani mai tsarki daga fitattun makaranta na duniyar musulmi, da nufin kara fadada ayyukan kur’ani a shafukan yanar gizo da ake ziyarta koina
782955