Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro na yin nazari kan mahangar addinin muslunci dangane da harkokin kudi da banki, wanda shi ne irinsa na farko da za agudanar a birnin Doha na kasar Qatar, da zai samu halartar masana kan harkokin kudi na kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, za a gudanar da wani zaman taro na yin nazari kan mahangar addinin muslunci dangane da harkokin kudi da banki, wanda shi ne irinsa na farko da za agudanar a birnin Doha na kasar Qatar, da zai samu halartar masana kan harkokin kudi na kasa da kasa, musamman daga kasashen musulmi da na larabawa.
Wani rahoton kuma ya habarta cewa, babban malami kuma mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi’a a kasar Lebanon ayatollah Abdulamir Qabalan ya kirayi mabiya addinan musulunci da kiristanci na kasar Lebanon zuwa ga hadin kai da fahimtar juna a dukkanin bangarorin da suka hada su na siyasa da kuma zamantakewa.
Malamin ya yi wannan kira ne a cikin wani sakon taya murna da ya aike wa jagoran mabiya addinin kirista na kasar Lebanon na zagayowar ranar easter, wadda mabiya addinin kirista suke girmamawa, ya kara kda cewa dukkanin addiunan biyu suna tarihin zama tare da fahimtar juna a tsakaninsu, a kan wajibi da ya rataya kan dukkanin mabiyansu a Lebanon sun yi koyi da tarihin addinan biyu.
788482