IQNA

Musulmin Kasar Tare Da Kiristoci Suna Yin Kira Zuwa Ga Hadin Kai Tsakaninsu

19:36 - May 15, 2011
Lambar Labari: 2122636
Bangaren kasa da kasa, dubban mabiya addinin muslunci ne tare da mabiya addinin kirista suka gudanar da gangami a dandalin tahrir da ke birnin alkahira fadar mulkin kasar Masar, domin tabbatar da hadin kai tsakanin dukkanin mabiya addinin biyu a cikin fadin kasar Masar, tare da kawo karshen sabanin addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo lemonde cewa, dubban mabiya addinin muslunci ne tare da mabiya addinin kirista suka gudanar da gangami a dandalin tahrir da ke birnin alkahira fadar mulkin kasar Masar, domin tabbatar da hadin kai tsakanin dukkanin mabiya addinin biyu a cikin fadin kasar Masar, tare da kawo karshen sabanin addini a tsakanin dukkanin al’ummar kasar Masar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata ne aka yi fama da rikicin addini, inda wasu da ake zaton cewa masu akidar kafirta sauran musulmi ne da suke samun goyon baya daga Saudiyya ne suka kai hari kan wuraren ibadar mabiya addinin kirista da ke birnin Iskandariya, lamarin da ya jawo tashin hankali mai tsanani.
Dubban mabiya addinin muslunci ne tare da mabiya addinin kirista suka gudanar da gangami a dandalin tahrir da ke birnin alkahira fadar mulkin kasar Masar, domin tabbatar da hadin kai tsakanin dukkanin mabiya addinin biyu a cikin fadin kasar Masar, tare da kawo karshen sabanin addini a kasar.
791071

captcha