IQNA

Mutanen Kasar Lebanon Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Al’ummar Palastinu

19:35 - May 15, 2011
Lambar Labari: 2122637
Bangaren kasa da kasa, dubban mutanen kasar Lebanon ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar palastinu, a sakamakon zalunci da dannniyar da suke fuskanta daga haramtacciyar kasar Isra’ila tsawon shekaru sama da sattin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, dubban mutanen kasar Lebanon ne suka gudanar da wata gagarumar zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar palastinu, a sakamakon zalunci da dannniyar da suke fuskanta daga haramtacciyar kasar Isra’ila tsawon shekaru sama da sattin, bayan da ‘yan mukin mallakar Birtaniya suka taimaka ma yahudawa wajen mamaye kasarsa.
A yau al’ummomin duniya da dama, musamman ma a kasashen musulmi da na larabawa, ana gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar palastinu, domin tunawa da cika shekaru da mamaye palastinu da yahudawan sahyuniya suka yi, a kasashen Masar da Syria kuwa an gangami ne da ake kira komawa zuwa palastinu.
791332


captcha