IQNA

Taron Komitin Dindindim Na Tattalin Arziki A Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi

Bangaren kasa da kasa: a karo na ashirin da bakwai komitin dindindim na tattalin arziki da kasuwanci a kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin da biyar zuwa ashirin da takwas ga watan Mihr a shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da za a gudanar a birnin Istambul.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a karo na ashirin da bakwai komitin dindindim na tattalin arziki da kasuwanci a kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar ashirin da biyar zuwa ashirin da takwas ga watan Mihr a shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da za a gudanar a birnin Istambul.Wannan taro zai yi nazari da binciken yadda tattalin arziki da kasuwanci yak e binkasa a tsakanin gwamnatoci da kasashe da al'ummominsu da ke cikin wannan kungiya ta hadin kan kasashen musulmi da ke yadda hulda ke bunkasa a tsakaninsu da sauran abukansu na duniya da kuma a f=dabra su yi dubi kan irin matsalolin da suke fuskanta da yadda za su magance su.


792674