IQNA

Za A Gudanar Da Taron Bankin Muslunci Bangaren Kasuwanci A Birnin Dubai

11:21 - June 04, 2011
Lambar Labari: 2133075
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taron bankin musulunci a birnin Dbai na kasar hadaddiyar daular larabawa, domin gabtar da muhimman abubuwa na sayarwa ga sauran kamfanoni da bankin ke samarwa a bangarensa na kasuwanci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo felminggulf cewa, za a gudanar da zaman taron bankin musulunci a birnin Dbai na kasar hadaddiyar daular larabawa, domin gabtar da muhimman abubuwa na sayarwa ga sauran kamfanoni da bankin ke samarwa a bangarensa na kasuwanci da saka hannayen jari.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro dai za agudanar da shi ne acikin watanni masu zuwa, domin kara karfafa sauran kamfanoni masu bukatar yin mu'amala tare da wannan bankin a bangarori daban-daban na harkokinsa musamman ma a cikin kasashen musulmi, da kuma masu manyan ofisoshinsu a birnin na Dubai.

Za a gudanar da zaman taron bankin musulunci a birnin Dbai na kasar hadaddiyar daular larabawa, domin gabtar da muhimman abubuwa na sayarwa ga sauran kamfanoni da bankin ke samarwa a bangarensa na kasuwanci da sauran ayyuka.

802787
captcha