Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka danganci harkokin aikin haji, wanda za agudanar a babbar jami’ar nan ta ummul kura da ke birnin Makka mai alfarma, tare da halartar malamai da kuma masana gami da malaman jami’oin kasar ta Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiya go-makka an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan muhimman batutuwa da suka danganci harkokin aikin haji, wanda za agudanar a babbar jami’ar nan ta ummul kura da ke birnin Makka mai alfarma, tare da halartar malamai da kuma masana gami da malaman jami’oin kasar.
A bangare guda kuma kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto wani rahoto daga shafin yanar gizo na islamtoday cewa, ma’atar kula da ayyukan leken asiri a haramtacciyar kasar Isra’ila ta bukaci da a daina watsa kiran salla a cikin masallatan birnin Qods, amma babban gamayyar kungiyoyi da cibiyoyin muslunci ta birnin Qods ta ki amincewa da hakan, tare da bayyana cewa wannan wani yunkuri na wuce gona da iri daga bangaren haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba.
803943