Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, duk da irin hankoron da masu raba kansu da addini suka yin a ganin cewa sun mayar da kasar Bangaladash maras akidar addini, amma har yanzu addinin muslunci ne dai ya wanzu a matsayin addinin kasa, kuma ga dukkanin alamu zai ci gaba da kasancewa hakan, saboda tsayin dakar al'ummar kasar.
Sai dai kuma wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar hadin kankasashen musulmi ta OIC an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro a birnin Istanbul na kasar turkiya, wanda ya yi nazari kan hanyoyi da za abi wajen bunkasa harkokin ilimi a duniyar muslmi, ta yadda za asamu ci gaba ta wannan fuska daida da sauran kasashen da suka samu ci gaba a duniya.
Rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut an bayyana cewa, wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Lebanon Malam Muhammadi a lokacin da yake kai wata ziyara wa jagoran kirista na kasar Lebanon Bushara Al-rai ya bayyana cewa, mabiya addinin kirista na kasar Iran suna samun hakkokinsu kamar sauran musulmin kasar ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu ba, duk kuwa da cewa adadinsu kadan ne matuka a kasar ta Iran.
Gudanar da wani zaman taro a birnin Istanbul na kasar turkiya, wanda ya yi nazari kan hanyoyi da za abi wajen bunkasa harkokin ilimi a duniyar muslmi, ta yadda za asamu ci gaba ta wannan fuska daida da sauran kasashen da suka samu ci gaba na da matukar muhimmanci ga kasashe.
813277