IQNA

Kungiyar Hizbullah A Lebanon Ta Yi Allawadai Da Rusa Makabartar Musulmi A Qods

17:17 - June 29, 2011
Lambar Labari: 2146716
Bangaren kas ada kasa, kungiyar gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta Hizbullah ta yi kakkausar suka kan rusa makabartar musulmi da ke birnin Qods, wadda daya daga cikin muhimman wurare na tarihi da ake girmamawa a kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo Arabic.upi, kungiyar gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta Hizbullah ta yi kakkausar suka kan rusa makabartar musulmi da ke birnin Qods, wadda daya daga cikin muhimman wurare na tarihi da ake girmamawa a kasar da ma sauran wurare.
a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut an bayyana cewa, wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kasar Lebanon Malam Muhammadi a lokacin da yake kai wata ziyara wa jagoran kirista na kasar Lebanon Bushara Al-rai ya bayyana cewa, mabiya addinin kirista na kasar Iran suna samun hakkokinsu kamar sauran musulmin kasar ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu ba, duk kuwa da cewa adadinsu kadan ne matuka a kasar ta Iran.
A bangare guda bayanin ya ci gaba da cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Auzbakistan ta gudanar da zama, domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci mabiya addinin muslunci na kasar, musamman ma matsalolin da suke fuskanta ta fuskacin karancin ilimi da sauransu.
816660
captcha