Bangaren kasa da kasa, babban malamin addini kuma makarncin kur’ani mai tsarki da Allah ya yi wa rasuwa a kasar Masar a cikin makon nan sheikh Abul ainain, ya kasance yana son halartar wuraren karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, babban malamin addini kuma makarncin kur’ani mai tsarki da Allah ya yi wa rasuwa a kasar Masar a cikin makon nan sheikh Abul ainain, ya kasance yana son halartar wuraren karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Iraki a lokacin da yake raye.
Daya daga cikin shugabannin babban kwamitin makaranta kur’ani mai tsarki a birnin Karbala mai alfarma Ali Khafaji ya bayyan acewa, babban shehin malamin ya kasance yana da niyar halartar taron karatun kur’ani mai tsarki da aka gudanar kasa da makonni uku da suka gabata a birnin mai lafarma, amma saboda rashin lafiya bai samu halartar ba, daga karshe kuma Allah ya karbi ransa.
Babban malamin addini kuma makarncin kur’ani mai tsarki da Allah ya yi wa rasuwa a kasar Masar a cikin makon nan sheikh Abul ainain, ya kasance yana son halartar wuraren karatun kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa a kasar Iraki garin Karbala mai alfarma.
817497