IQNA

Taimakon Da Bangaren Gwamnati Ke Bayarwa Shi Ne Gimshikin Cigaban Harkokin Kur'ani

12:13 - July 06, 2011
Lambar Labari: 2149969
Bangaren kasa da kasa :Taimakon da bangaren gwamnati ke bayarwa yana daya daga cikin muhimman dalili da ke taimakawa a ci gaban da bangaren harkokin kur'ani ke samu kuma hakan yana karawa wannan bangare karfin guiwa matuka gaya.



Kamfanin dillancin Labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Taimakon da bangaren gwamnati ke bayarwa yana daya daga cikin muhimman dalili da ke taimakawa a ci gaban da bangaren harkokin kur'ani ke samu kuma hakan yana karawa wannan bangare karfin guiwa matuka gaya. Salah Habib Mahmud wakili daga kasar Iraki day a halarci gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa koro na ashirin da takwas a nan Birnin Tehran na jamhuriyar musulunci ta Iran a wata tattaunawa day a yi da kamafanin dillancin labaran Kur'ani na Ikna ya yi wannan bayani tare da jinjinawa bangaren gwamnati kan su ci gaba da taimakawa a wannan bangare.

819976
captcha