Bangaren kur’ani, an bude wasu cibiyoyi na koyon karatun kur’ani mai tsarki a birnin San’a fadar mulkin kasar Yemen, wanda cibiyar kula da ayyukan addini ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa tare da hadin gwiwa da cibiyoyin shirya karatun kur’ani na bazara.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an bude wasu cibiyoyi na koyon karatun kur’ani mai tsarki a birnin San’a fadar mulkin kasar Yemen, wanda cibiyar kula da ayyukan addini ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa tare da hadin gwiwa da cibiyoyin shirya karatun kur’ani na bazara kamar a kowace shekara a kasar ta Yemen.
babban daraktan kungiyar ta bunkasa harkokin al’adu da ilimi ta kasashen musulmi ta ISESCO ya bayyana cewa dole ne kasashen musulmi su yi la’akari da muhimmancin rawar da matasa suke takawa a bangarorin daban-daban na siyasa da rayuwar zamantakewar al’ummar musulmi da ma sauran al’ummomi.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar sabil an bayyana cewa, an gudanar da wani zaman taro mai taken kare qods hakki ne na dukkanin al’umma kuma hakan yana cikin ‘yan adamtaka, wanda cibiyar bunkasa al’adu muslunci ta kasar Jordan ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa tare da halartar masana dada kasashen duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na da matukar muhimmanci ga matasana kasar Gambia da aka san su da mayar da hankali a kan lamurran da suka danganci addini, ya ci gaba da cewa da dama daga cikin masu bindiddigin lamurra suna ganin cewa bude wannan cibiya zai kara karfin matasa masu sha’awar karatun kur’ani.
825104