IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi OCI Ta Taya Musulmi Murnar Shiga Watan Ramadan

11:36 - August 02, 2011
Lambar Labari: 2163837
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta OCI ta taya dukkanin musulmin duniya shiga watan Ramadan mai afarma ta hanayr fitar da wani bayani da bababn sakataen kungiyar Ikmaluddin Iglo ya yi a jiya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, kungiyar kasashen musulmi ta OCI ta taya dukkanin musulmin duniya shiga watan Ramadan mai afarma ta hanayr fitar da wani bayani da bababn sakataen kungiyar Ikmaluddin Iglo ya yi a jiya kamar dai yadda rahoton ya bayyana.

A cikin bayanin Auglo ya bayyana cewa; suna taya dukkanin muslmin duniya murnar shiga wannan wata mai albarka, wanda rahmar Allah madaukain sarki take safka a cikinsa akan bayinsa, inda ya ce wata na ibadar Allah tare da kiyaye kai daga aikata duk wani abun zai kai mutum zuwa ga sabonsa madaukin sarki.

Y ace dole ne al'ummar musulmi ta yi amffani da wannan damar wajen karfafa hadin kai da fahimtar juna da ke akwai atsakanin dukkanin 'ya'yanta, tare damayar da hankali ga muhimman abubuwa da musulunci yake da matukar bukatuwa zuwa gare shi daga mabiyansa a wannan zamani da muke rayuwa a cikinsa a duniyarmu ta yau.

Kungiyar kasashen musulmi ta OCI ta taya dukkanin musulmin duniya shiga watan Ramadan mai afarma ta hanayr fitar da wani bayani da bababn sakataen kungiyar Ikmaluddin Iglo ya yi a jiya ga dukkanin gwamnatoci na kasashen musulmi baki daya.

835642

captcha