IQNA

Wilayat Faqih A Lokacin Babbar Fakuwa Ita Ce Ke Rike Da Tuta

19:00 - September 07, 2011
Lambar Labari: 2183368
Bnagaren kasa da kasa, daraktan cibiyar ilmi ta kasa baki daya ya bayyana cewa jibinta lamari ga malami masani wato wilayat Faqih ita ce ke rik eda tutar shiriya a lokacin babbar fakuwa ta limami ma'asumi.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa daraktan cibiyar ilmi ta kasa baki daya ya bayyana cewa jibinta lamari ga malami masani wato wilayat faqih ita ce ke rike da tutar shiriya a lokacin babbar fakuwa ta limami ma'asumi ga mabiya tafrakin iyalan gidan manzon Allah.

Abin takaici ne cewa wasu mabiya addinan da ba su da cikakkiyar masaniya akan koyarwar addini, suna zaton cewa suna da matsayi na musamman a wurin Ubangji, kuma da su kadai ne Ubangiji ya damu, kuma saboda su kadai ne ya aiko annabawa, saboda haka ba a shirye su ke ba su yi imani da wasu annabawa kuma ba su cikin masu yi musu biyayya.
Allah madaukakin sarki ba shi da dangantaka da wata kabila ko da wasu iyalai domin kuwa a wurin kowa da kowa daidai wa daida su ke. Abu guda daya wanda ya ke sa mutane su kusance shi ko su yi nisa da shi shi ne aikin da su ke yi, kuma kowane mutum aiki da ya yi ne yake bibiyyarsa.
Shakka babu aikin da ya ke zama karbabbe shi ne wanda aka yi da tsarkin niyya saboda Allah, domin kuwa wannan irin aikin yana nuni ne da imani na hakika da kuma nesantar duk wani nau'i na shirka.
Wannan ayar tana yin nuni ne da cewa halin mutum na son ya mallaki kowai ya kai shi ga nuna cewa Ubangiji ma yana tare da shi ne shi kadai, ba waninsa ba.
Yana daukar cewa Ubangiji nashi ne shi kadai ba na waninsa ba, alhali kuwa shi Ubangiji bai kebanta mabiyan wani addini ne ko wata zuriya ko wata kabila ba, Ubangiji na dukkanin talikai ne.
855734
captcha