IQNA

Amurka Na Kokarin Hawan Kojerar Naki Domin Hana Kafa Kasar Palastinu

20:39 - September 19, 2011
Lambar Labari: 2190187
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da al’ummomin kasashen musulmi da na larabawa suke yin bore domin neman ‘yanci da sauyi na siyasa, a nata bangaren Amurka tana kai gwabro ta kai mari hana kafa kasar Plastinu mai cin gishin kanta.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto rahoto daga shafin sadrawa na yanar gizo na MA’A cewa, wakiliyar kasar Amurka kwamitin tsaron majalisar dinin duniya Susan Rice ta fito kara ta nuna adawarsu da kafa kasar mai cin gishin kanta mai suna palastinu, inda ta sha alwashin yin amfani da hakkin hawa kujerar naki wajen kin amincewa da wannn yunkurin na palastinawa a kwamitin tsaro, ko da kuwa dukkanin kasashe sun amince da hakan.
A daidai lokacin da al’ummomin kasashen musulmi da na larabawa suke yin bore domin neman ‘yanci da sauyi na siyasa, a nata bangaren Amurka tana kai gwabro ta kai mari hana kafa kasar Plastinu mai cin gishin kanta, kuma tun kafin lokacin da dama ta sanar cewa ba zata tab amincewa da duk mataki makamancin haka ba.
Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya dai na kujeru 15 ne a matsayin mambobinsa, biyar daga cikinsu wato Amurka, China, Rahsa, da kuma Birtaniya da Faransa su ne mambobi na dindin, sauran goma kuma ana zabarsu daga sauran sassa na kasashen duniya.
862948






captcha