Yayin da Arbaeen ke gabatowa, hanyoyin da ke fadin kasar Irakin da suka kai birnin Karbala suna cike da maukibi na masu aikin sa kai wadanda ke ba da agajin abinci, ruwa, wuraren hutawa, da magunguna ga masu ziyara daga wurare masu nisa.
Ranar Arbaeen ta cikar kwanaki 40 ne bayan Ashura, ranar shahadar Imam Husaini (AS), jikan Manzon Allah (SAW). Ziyarar arba’in na jan hankalin miliyoyin mutane a kowace shekara, da dama daga cikinsu suna tafiya da kafa na tsawon daruruwan kilomitoci domin nuna kaunarsu ga wannan imami jikan manzon Allah (SAW).
A wannan shekara, lokacin ziyarar Arbaeen ya fado ne a ranar 14 ga watan Agusta. Maziyarta kan fara tafiya zuwa Karbala kusan makonni biyu a gaba.
A bara, fiye da mutane miliyan 20 ne suka halarci taron ziyarar arbaeen, a cewar hukumomin Iraki , wanda ya zama babban taron addini na shekara-shekara a duniya.