IQNA

Ganawar Ministan Harkokin Wajen Masar Da Sakataren Kungiyar Kasashen Musulmi

13:59 - October 04, 2011
Lambar Labari: 2198891
Bangaren kasa da kasa, ministan harkokin wajen kasar Masar Muhammad Amru ya gana da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ikmaliddin Auglo a birnin Alkahira na kasar Masar dangane da abubuwan da uke da komowa a yankin gabas ta tsakiya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jariidar yaum Al-sabi ta kasar Masar cewa, a jiya ministan harkokin wajen kasar Masar Muhammad Amru ya gana da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ikmaliddin Auglo a birnin Alkahira na kasar Masar dangane da abubuwan da uke da komowa a yankin gabas ta tsakiya da ma wasu daga cikin kasashen musulmi.
Zaaman tattaunawar ya yi tsokaci kan wasu daga cikin muhimman lamurra da suka danganci matsayin kungiyar a kan abubuwan da sukefaruwa a cikin kasashen larabawa, inda kungiyar ke ganin ya kamata a saurari abubuwan da mutane suke kokawa a kansu, domin warware matsalolinsu, ta yadda za a samu zaman lafiya tsakanin al’umma.
Haka nan kuma sun yi dubi dangane da zaman da kungiyar za ta gudanar, wanda zai kunshi mambobinta baki daya daga kasashen musulmi, da kuma masu sanya ido daga kasashen turai da na Afirka da ma yankin latin, kuma zaman zai gudana ne a cikin wannan shekara a kasar Masar.
ministan harkokin wajen kasar Masar Muhammad Amru tare da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ikmaliddin Auglo, sun jaddada muhimmancin mayar da hanakali wajen bunkasa lamurran kungiyar musamman a cikin wannan lokaci.
872497
captcha