Bangaren kasa da kasa:kimanin masu zanga zanga dari da saba'in ne daga cikin wadanda suka fito a ranar ashirin da hudu ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka yi awangaba da su a kasashe daban daban kama daga Amerika har Ostriya saboda sun halarci zanga-zangar nuna kama day an jari hujja kuma yan sanda ne suka kama su da yin awangaba da su.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kimanin masu zanga zanga dari da saba'in ne daga cikin wadanda suka fito a ranar ashirin da hudu ga watan Meher na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka yi awangaba da su a kasashe daban daban kama daga Amerika har Ostriya saboda sun halarci zanga-zangar nuna kama day an jari hujja kuma yan sanda ne suka kama su da yin awangaba da su.Wannan kamu da yin awangaba da aka yi wa wadanda suka fito don nuna adawarsu da zaluncin yan jari Hujja a Amerika ya maida hannun agogo baya zuwa lokacin yakin da Amerika ta kai wa Vetnam a shekara ta dubu daya da dari tara da sattin da takwas inda dubban yan kasar Amerika a lokacin suka gudanar da zanga-zangar adawa da wannan yaki amma aka kama wasu daga cikinsu.
881291