IQNA

19:00 - November 19, 2011
Lambar Labari: 2224859
Bangaren kasa da kasa, mataimakin bababn sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Sheikh Na'im Kasim ya bayyana cewa, gwagwarmay da zalunci ita kadai ce hanyar samun nasar kan azzalumai da kuma rusa makircin makiya.Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin dil Al-manar ta kasar Lebanon cewa, mataimakin bababn sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Sheikh Na'im Kasim ya bayyana cewa, gwagwarmay da zalunci ita kadai ce hanyar samun nasar kan azzalumai da kuma rusa makircin makiya da suke kitsa makirci ga addinin muslunci da musulmi.

Sheikh Na'im Kasim ya bayyana hakan en a lokacin da yake ganawa da jakadan kasar Sudan a kasar Lebanon a wata ziyara da ya kai masa, a lokacin da suka tabo batun matsalar siyasa da ake fama da ita a cikin kasar Syria, wadda kasasahen turai suka shirya kuma wasu daga cikin kasashen larabawa suke aiwatar da hakan.

A jiya ne ministan harkokin wajen kasar Syria Walid mu'allim ya gudanar da wani taron manema labarai a birnin Damascus fadar mulkin kasar, taron da ya samu halartar wakilai na kafofin yada labarai na cikin gida da kuma kasashen ketare.
A wannan zaman taro Walid Mu'allim ya bayyana matsayin gwamnatin Syria dangane da matakin da kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta dauka na dakatar da Syria a matsayinta na mamba a kungiyar, inda ya bayyana cewa matakin ya sabawa dukkanin ka'idoji da aka kafa kungiyar a kansu, wanda kuma Syria na kan gaba wajen kafa wannan kungiya.
Ya ce Syria tana da cikakkiyar masaniya dangane da abin da aka shirya na makarkashiya a kanta a zaman taron kungiyar kasashen larabawa, amma duk da haka tana fatan larabawan za su koma cikin hankalinsu, domin aiwatar da abin da yake daidai, domin warware matsalolin da kasar Syria take fama da su, da hakan ya hada da dakatar da bayar da makudan kudade ga kungiyoyin 'yan ta'adda da suke kai hare-hare a kan jami'an tsaro da fararen hular Syria, wanda ya ce wasu daga cikin kasashen larabawan yankin tekun fasha ne ke da alhakin hakan, da kuma dakatar da shigo da makamai zuwa ga 'yan ta'addan daga kasar Turkiya.
900181
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: