IQNA

An Zabi Birnin Najaf A matsayin Birnin Tattaunawar Addinai A Shekara Ta 2014

18:09 - November 22, 2011
Lambar Labari: 2227125
Bangaren kasa da kasa, an zabi birnin Najaf mai alfarma amatsayin birnin tattaunawar addinai acikin shekara ta 2014 kamar kwamitin kula da harkoin ilimi da bunkasa al’adu a kungiyar kasashen musulmi ya bayyana.
Kamfanin dillanin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyarbunkasa al’adu ta Al-salah cewa, an zabi birnin Najaf mai alfarma amatsayin birnin tattaunawar addinai acikin shekara ta 2014 kamar kwamitin kula da harkoin ilimi da bunkasa al’adu a kungiyar kasashen musulmi ya bayyana a cikin wani bayani da aka ftar kan wannan batu.
A wani labarin kuma, al'ummar kasar Bahrain na ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman kawo sauyi a cikin kasar, a wani rahoto na tashar telbijin din cnn wanda ta ambato shedun ganin ido, na nuni da cewa zanga-zangar da mutanen kasar ke yi na kara kaimi bayan da jami'an tsaro su ka kashe wani matashi ta hanyar take shi da mota.

A yayin jana'izar matashin wacce dubun dubatar masu zanga-zangar su ka halarta an sake yin wani taho mu gama din da jami'an tsaro da su ka yi amfani da hayaki mai sa hawaye,tun a cikin watan Febrairu ne dai al'ummar kasar ta Bahrain su ka fara gudanar da zanga-zanga ta neman a kawo sauyi a cikin tsarin siyasar kasar na mulukiya da maida shi jamhuriya.
902433


captcha