Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadrawa na yanar gizo na tashar talabijin dil Aljazeera cewa, sakatatren kwamitin malaman muslulmi na duniya Yusuf Qardawi ya kirayi gwamnatin Jordan wadda take dasawa da haramtacciyar kasar Isra’ila da ta hana yahudawan sahyuniya rusa kofar magariba a masallacin Qods mai alfarma.
Yusuf Qardawi ya kirayi gwamnatin Jordan saboda tana dasawa da Haramtacciyar kasar Isra’ila, amma kuma a lokaci guda ya bar masarautar Qatar wadda ita ce babbar mai yima yahudawa aikia halin yanzu a yankin gabas ta tsakiya baki daya.
Kwamitin malaman addinin muslunci na duniya ya yi kira da a kai dauki ga masallacin Qods da yahudawan sahyuniya ke shirin rusawa tare da sauran wurare masu tsarki da suke cikin birinin Akasa mai alfarma da kuma mamaye kaddaroron al’ummar musulmi na palastinu
Qardawi ya kirayi gwamnatin Jordan wadda take dasawa da haramtacciyar kasar Isra’ila da ta hana yahudawan sahyuniya rusa kofar magariba, saboda wannan kofar ce da musulmi suke shiga cikin masallacin ta hanayarta domin yin ibada.
904780