IQNA

Zaman taron Masu Sanya Ido Kan Palastinawa ‘Yan Gudun Hijira A Birnin Alkahira

20:04 - January 30, 2012
Lambar Labari: 2265154
Bangaren kasa da kasa, an kafa wani kwamiti na bincike kan harkokin palastinawa ‘yan gudun hijira wanda zai gudanar da zamansa a birnin Alkahira na kasar Masar a cikin wannan mako a babban ginin kungiyar hadin kan kasashen larabawa.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-dastur ta kasar Jordan cewa, an kafa wani kwamiti na bincike kan harkokin palastinawa ‘yan gudun hijira wanda zai gudanar da zamansa a birnin Alkahira na kasar Masar a cikin wannan mako a babban ginin kungiyar hadin kan kasashen larabawa da ke cikin birnin.
A wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dilalncin labaran iqna, shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa kamar yadda suka shirya.
Kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
942515


captcha