IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Rufe Kofar Shiga Masallacin Qods Domin Hana Salla

19:56 - February 13, 2012
Lambar Labari: 2273581
Bangaren kasa da kasa, sojojin yahudawan sahyuniya sun rufe kofar shiga masallacin Qods domin hana palastinawa yin sallah a cikinsa hakan ya zo ne a wani mataki da mambobin jamiyar likud ta masu tsatsauran ra’ayi daga cikinsu ta dauka domin tsokanar musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, y naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a yau yahudawan sahyuniya sun rufe kofar shiga masallacin Qods domin hana palastinawa yin sallah a cikinsa hakan ya zo ne a wani mataki da mambobin jamiyar likud ta masu tsatsauran ra’ayi daga cikinsu ta dauka domin tsokanar musulmi mazaunan birnin, da sauran musulmi masu sauran lamiri a cikin kasashen musulmi da na larabawa.
A wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dilalncin labaran iqna, shugaban majalisar muslunci mai kula da ayyukan da suka danganci batun ‘yantar da palastinu daga mamayar yahudawa Muhammad Namir ya sheda cewa, gwagwarmayar muslunci ce ta hana mayar da birinin Qods mai alfarma babban birnin yahudawa kamar yadda suka shirya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
Kungiyar ta hizbullah a kasar Lebanon ba ya ga kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar, ta kirayi iriin wadannan manafukan larabawa da su sake yin nazari kan makomarsu bisa la’akari da halin da ake ciki yanzu haka a yankin.
952013

captcha