IQNA

An Yi Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Rashin Amincewa Da Keta Alfar Kur'ani Afghanistan

16:51 - February 22, 2012
Lambar Labari: 2279112
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane sun fito kan manyan titunan birnin Kabul na kasar Afghanistan domin nuna rshin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamaya suka yi a cikin 'yan kwanakin nan.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo dawn cewa, dubban mutane sun fito kan manyan titunan birnin Kabul na kasar Afghanistan domin nuna rshin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamaya suka yi a cikin 'yan kwanakin nan lamarin day a fusknacin fushin al'ummar musulmi na kasar.
Rahotanni daga kasar Afghanistan sun habarta cewa akalla sojojin kungiyar tsaro ta Nato uku ne suka rasa rayukansu a yau bayan da wata nakiya ta tashi da su a yankin kudancin kasar.
Mai aiko ma gidan talabijin din Al-alam rahotanni daga birnin Kabul na kasar Afghanistan ya bayyana cewa, sojojin mamayar uku sun halaka ne bayan da motar da take dauke da su ta taka nakiyar da aka bizne a kan hanyarsu a wani yanki da suke sintiri a kudancin kasar.
A bangare guda kuma wani farar hula guda ya rasa ransa wasu kimanin 20 kuma sun jikkata a lokacin da dubban mutane suke gudanar da zanga-zanga a yau a birnin Kabul fadar mulkin kasar, domin nuna fushinsu kan keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka suka yi a kasar.
957705

captcha