Bangaren kasa da kasa, daliban hauzar Najaf ashraf da ke kasar Iraki, sun nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka da ke kasar afghansiatan suka yi, tare da kiran dukaknin musulmi da su dauki matakan da suka dace na mayar da martini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iba cewa, daliban hauzar Najaf ashraf da ke kasar Iraki, sun nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da sojojin mamayar Amurka da ke kasar afghansiatan suka yi, tare da kiran dukaknin musulmi da su dauki matakan da suka dace na mayar da martini kan wannan babbar ta'asa da makiya suka aikata.
Daya daga cikin wadanda suka gudanar da wannan zanga-zanga wanda kuma darakta na wata cibiyara ddini mai zaman kanta abirnin Najaf Kazim jabiri ya bayyana cewa, babbar manufar gudanar da wannan gangami it ace tabbatar wa duniya cewa, musulmi ba za su zura ido suna kallon abin da ke faruwa na keta alfarmar kur'ani da makiya musulunci ke yi ba.
A cikin 'yan makonnin da suka gabata ne wasu daga cikin sojojin mamayar Amurka suka kone kur'ani mai tsarki a kasar Afghanistan, a wani mataki na tsokanar mabiya addinin muslunci da ke fadin duniya, lamarin da ya fuskanci mayar da martini daga kasashen musulmi da dama, musamman masu lamiri da 'yancin siyasa daga cikinsu.
968304