IQNA

Gidan radiyon Kur'ani Na Birnin Alkahira Ya Cika Shekaru 48 Da Kafawa

13:58 - March 26, 2012
Lambar Labari: 2294843
Bangaren kasa da kasa, gidan radiyon kur'ani na birnin Alkahira na kasar Masar ya cika shekaru arba'in da takwas cur da budewa, kuma yana ci gaba da gudanar da shirinsa mai kayatarwa da farin jinni tsakanin al'ummar kasar da ma kasashen ketare.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum Sabi cewa, gidan radiyon kur'ani na birnin Alkahira na kasar Masar ya cika shekaru arba'in da takwas cur da budewa, kuma yana ci gaba da gudanar da shirinsa mai kayatarwa da farin jinni tsakanin al'ummar kasar da ma kasashen ketare musamman na larabawa daga cikinsu.
Wannan gidan radiyo dai yan adaga cikin gidajen radiyo masu farin jinni da karbuwa atsakanin masu saurare a cikin kasashen larabawa, wanda kuma ya taka gagarumar rawa wajen fadakar da kan mutane domin komawa zuwa ga koyarwar kur'ani mai tsarki a cikin harkokin rayuwar jama'a ta zamantakewa.
Gidan radiyon kur'ani na birnin Alkahira na kasar Masar da ya cika shekaru arba'in da takwas cur da budewa, kuma yake ci gaba da gudanar da shirinsa mai kayatarwa da farin jinni tsakanin al'ummar kasar, ya samu kyautuka da dam adaga cibiyoyi na kasa da kasa da kuma kasashen musulmi saboda kokarin da yake yi.
974996
captcha