Kamfanin dilalncin labaran qina ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam Today cewa, gungun lauyoyi musulmi sun gudanar da wani zama na musamma a birnin maskat fadar mulkin kasar Oman domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa domin kare hakkokin fararen hula.
Daga cikin wadanda suka halarci taron har da wakilai daga kasashen Iran, Yeman, Saudiyya, Lebanon, Morocco, Tunisia, Turkiya, Aljeria, Libya, Oman da kuma Qatar, wadanda dukakninsu mambobi ne akungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, wadda ta take wakiltar musulmi a taruka na kasa da kasa.
Kungiyar lauyoyi musulmi sun gudanar da wani zama na musamma a birnin maskat fadar mulkin kasar Oman domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa domin kare hakkokin mutane, duk kuwa d cewa ra’ayoyi kan boren larabawa sun sha banban.
980554