IQNA

Fara Wani Babban Zangon Koyar Da Kur'ani Mai Taken Jami'atul Kur'ani A Kabul

17:52 - April 23, 2012
Lambar Labari: 2311034
Bangaren harkokin kur';ani mai girma:Cibiyar da ke koyar da kur'ani mai girma ta jami'atul Kur'ani a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan ta farad a kaddamar da wani babban tsari da shiri na koyar da kur'ani mai girma a wannan sheka ga al'ummar kasar.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Cibiyar da ke koyar da kur'ani mai girma ta jami'atul Kur'ani a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan ta farad a kaddamar da wani babban tsari da shiri na koyar da kur'ani mai girma a wannan sheka ga al'ummar kasar.Wannan cibiya tana daya daga cikin manya kuma shahararrun cibiyoyin koyarwa da bada horo na kr'ani da ilimomin da suka shafi addinin musulunci a fadin kasar ta Afganistan kuma tana gudanar da ayyukanta ne a yankuna daban daban na wannan kasa kuma tana da ku=imanin ajijiwa goma sha uku na koyar da kur'ani mai girma a birnin Kabul kawai kuma ya talibai kimanin dari uku ke daukan darasi a gurin .
990791
captcha