IQNA

Fara Taron Karawa Juna Sani Kan Tafsirin Kur'ani Mai Girma A Afrika Ta Kudu

16:50 - April 29, 2012
Lambar Labari: 2314477
Bangaren kasa da kasa; taron karawa juna sani kan tafsirin kur'ani mai girma da aka fara a yau tara ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin KipTon fadar mulkin kasar ta Afrika ta kudu.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: taron karawa juna sani kan tafsirin kur'ani mai girma da aka fara a yau tara ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin KipTon fadar mulkin kasar ta Afrika ta kudu.An nakalto daga majiyar labarai ta ctme.co.za cewa; wannan taron karawa juna sani da cibiyar koyar da ilimin addinin musulunci a Afrika ta kudu ta shirya da daukan dawainiyarsa da zummar kara fadakar da musulmi sanin ilimin addini da tafsirin kur'ani mai girma da kuma shinfida hanya da yayani na habaka harkokin ilimin addini da koyarwa a wannan kasa .Kuma yawancin musulmi ne suka samu halartar wannan taron karawa juna sani kan tafsirin kur'ani da kuma suka bayyana gamsuwa da jin dadinsu kan wannan mataki da kuma salon a fadakarwa da ilmantar da musulmin wannan kasa ta Afrika ta kudu.Kuma malamai dam asana goma ne suke jagorantar wannan taron karawa juna sani kan tafsirin kur'ani mai girma kuma za a ci gaba da gudanar das hi har zuwa yau goma ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya.

994622
captcha