Bangaren kasa da kasa, masani kan harkokin yankin gabas ta tsakiya dan asalain kasar Birtaniya ya tabbatar da cewa, mahukuntan kasar Bahrain suna nuna wariya da banbamci tsakanin mutanen kasar wadanda aka sarinsu mabiya tafarkin shi’a ne da kuma marassa rinjaye masu wadanda gidan sarautar ke komawa gare su.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, masani kan harkokin yankin gabas ta tsakiya dan asalain kasar Birtaniya ya tabbatar da cewa, mahukuntan kasar Bahrain suna nuna wariya da banbamci tsakanin mutanen kasar wadanda aka sarinsu mabiya tafarkin shi’a ne da kuma marassa rinjaye masu wadanda gidan sarautar ke komawa gare su tare da taimakon gwamnatin wahabiyawan Saudiyya da kasashen yammacin turai.
Mahukuntan kasar Bahrain sun kama shugaban cibiyar kare hakkin bil adama mai zaman kanta a kasar Nabil Rajab bisa hujjar cewa yana yin kalaman da suke tunzura jama'a domin su yi zanga-zangar bore ga gwamnatin kasar.
Jami'an tsaron kasar ta Bahrain sun kama Nabil Rajab jiya a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Manama, a lokacin da yake fitowa daga cikin jirgi bayan dawowarsa daga wani zaman taro na kungiyoyin kare hakkin bil adama da aka gudanar a birnin Beirut na kasar Lebanon, inda suka yi awon gaba da shi ba tare da yi masa wani bayani ba.
A karshen watan Afirilun da ya gataba ma mahukuntan na kasar Bahrain sun kame Nabil Rajab, bisa hujjar shiga zanga-zangar nuna goyon baya mai fafutukar kare hakkokin bil adama Abdulhadi Khawajah, wanda ke yajin cin abinci kuan watanni uku a jere a gidan kurkukun da ake tsare da shi.
1000873